Da dumi dumi: An gano wasu gawarwarki da suka fara rubewa a ciki baraguzan gidan daya fadi a Abuja

Da dumi dumi: An gano wasu gawarwarki da suka fara rubewa a ciki baraguzan gidan daya fadi a Abuja

A garin bincike bincike, an gano wasu gawarwaki a cikin baraguzan wani babban gidan sama hawa hudu daya ruguje a babban birin tarayya Abuja a ranar Juma’ar data gabata, sai dai gawarwakin sun fara rubewa, inji rahoton jaridar TheCables.

Jami’an hukumar bada agajin gaggawa ne suka fara gano gawarwakin da misalin karfe 10:50 na safiyar Litinin 20 ga watan Agusta, yayin da suke kokarin kwashe baraguzan ginin, kamar yadda majiyar NAIJ.com ta ruwaito.

KU KARANTA: Babbar Sallah: Matar Gwamna Kashim Shettima ta yi rabon raguna 100 ga Malamai da gajiyayyu

Sai dai kafin a ankara, yan uwan mamacin sun tinkaro wajen, inda suka mamaye ma’aikatan suna yi ma jami’an hukumar tofin Allah tsine tare da kalubalantarsu akan wani dalili suka kasa ceto dan uwan nasu.

Da dumi dumi: An gano wasu gawarwarki da suka fara rubewa a ciki baraguzan gidan daya fadi a Abuja

Neman gawarwakin

Aiki yayi nisa na kwashe gawarwakin zuwa lokacin da majiyarmu ta hada wannan rahoto. Sai dai yayin da shugaban karamar hukumar Abuja, Umar Shuaibu ke cewa gawar mutum daya suka gani, sai kuma wadanda aka ceta, su kuwa matasan unguwar cewa suka yi akwai mutane 18 a karkashin ginin.

A wani labarin kuwa, wani matashi dake tuka Keke Napep yace akwai yan uwansa guda biyu da hatsarin ya rutsa dasu, inda yace kaninsa Aliu mai shekaru 23 da yayansa Ali Mohammed mai shekaru 30 sun tsallake rijiya da baya.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar NAIJ.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.naij.com

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.naija.ng

Related news
Jahilci: An gano wata kabila a Najeriya da har yanzu ke sayar da ‘ya’ya mata

Jahilci: An gano wata kabila a Najeriya da har yanzu ke sayar da ‘ya’ya mata

Jahilci: An gano wata kabila a Najeriya da har yanzu ke sayar da ‘ya’ya mata
NAIJ.com
Mailfire view pixel