Huduba Ta Sha takwas

Daga cikin kalamansa (A.S) game da zargin malamai akan bayar da fatawa. Acikinta ne yake sukan masu bayar da fatawa da ra’ayoyinsu. Kuma yana mai jingina al’amuran hukunci na addini ga kur’ani

Wata fatawa takan zo wa waninsu na hukunce-hukunce sai ya yi hukunci a cikinta da ra’ayinsa, sannan sai wata ta sake zuwa irinta sai ya yi wani hukunci sabanin abin da ya fada a baya, sannan sai a tara masa alkalai gun shugabansu da ya sanya su kan al’amarin hukunci sai ya karbi ra’ayoyinsu gaba daya, ubangijinsu daya! Annabinsu daya! Littafinsu daya!

Shin Allah (S.W.T) ne ya umarce su da sabani sai suka bi shi! Ko kuma ya yana su ne sai suka saba masa! Ko kuwa Allah (S.W.T) ya saukar da addini tauyayye ne sai ya nemi taimakonsu kan cika shi! Ko kuwa su abokan tarayya ne nasa don haka sai su fadi abin suka ga dama shi kuma dole ya yarda? Ko kuwa Allah ya saukar da addininsa cikakke ne sai annabi (S.A.W) ya takaita wajen isar da shi? Allah (S.W.T) kuma yana cewa: (babu wani abu da muka bari a littafi) a cikinsa kuma akwai bayanin komai, kuma ya ambaci cewa littafinsa wani bangare yana gaskata wani bangare, kuma babu wani sabani a cikinsa, sai madaukaki ya ce: (da ya kasance daga wajen wanin Allah da an samu sabani mai yawa a cikinsa).

Kuma alkur’ani zahirinsa mai kayatarwa ne, kuma badininsa mai zurfi ne, mamakinsa ba ya karewa, kuma kayatarwarsa ba ta karewa, kuma ba a yaye duhu sai da shi.