An cafke wanda ake zargi da kai hari a Faransa

Shekara guda kenan tun bayan wasu masu ikirarin kishin Islama suka hallaka mutane 130 a birnin Paris Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Shekara guda kenan tun bayan wasu masu ikirarin kishin Islama suka hallaka mutane 130 a birnin Paris

Hukumomi a Morocco sun kama wani mutum wanda suke zargin yana da hannu a wani yunkurin kungiyar IS na kai hari a Faransa.

Sun ce mutumin, ya hadu da mayakan IS a kan iyakar Turkiya da Syria, inda suka ba shi sakon umurni da zai gabatar wa wani gungun masu ra'ayi irin na kungiyar.

'Yan sandan Faransa sun ce gungun mutanen ya tarwatse ne bayan an kama mutane bakwai 'yan asalin Faransa da Morocco da Afghanistan a watan Nuwamba.

Har yanzu, Faransa na cikin shirin ko ta kwana ne tun bayan hare-haren masu da'awar kishin Islama da ta fuskanta a baya.