in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Namibia ya kara mata a majalissar zartaswa
2018-02-13 20:08:12 cri
Shugaban kasar Namibia Hage Geingob, ya maye gurbin wasu mataimakan ministocin kasarsa da mata, a wani mataki na yiwa majalissar zartaswar kasar garambawul, bayan da a makon jiya ya sauya wasu daga ministocin kasar.

Karkashin shirin yiwa majalissar zartaswar kasar ta Namibia garambawul, shugaba Geingob ya dauki matakai na daidaita yawan kujerun mataimakan ministocin bisa lura da jinsinsu, kamar dai yadda wata sanarwa da ofishin fadar shugaban kasar ta bayyana.

Bisa wannan aniya dai, yanzu haka yawan mata masu rike da mukamin mataimakan ministocin kasar ya kai 17, baya ga maza 11 da ake da su. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China