Connect with us

BABBAN BANGO

Labarin Amina Du, Wakiliyar Hausa Ta Farko Da Radiyon CRI Ya Tura Nijeriya

Published

on


A shekaru 10 da suka gabata, idan an tambaye ni dalilin da ya sa nake koyon wani harshe na nahiyar Afrika, ko zan je Afrika? Ban san yadda zan amsa wannan tambaya ba, amma yauzu, na kwashe shekara daya da rabi ina aiki a Nijeriya, ina da labarai da dama da zan bayar game da Nijeriya, taken wadannan labarai shi ne “Labaran ‘yar jaridar kasar Sin a Nijeriya.”
Tambaya ta farko: A ina ne kika koyi harshen Hausa?
Lokacin da na isa Abuja, idan na yi magana da mutane da harshen Hausa, sai su yi ta mamaki, suna cewa: kai ga wata basiniya tana magana da Hausa kamar bahaushiya, kusan kowa yana yi mini wannan tambaya: A ina kika koyi harshen Hausa?
Amsa:
Na koyi karshen Hausa a wata jami’ar dake birnin Beijing, inda na karanta harshe da al’adun hausa “Hausa Lauguage and Literature” a turance. Na yi shekaru hudu a jami’a ina koyon harshen Hausa. Yanzu haka akwai jami’o’i biyu a nan kasar Sin dake koyar da harshen Hausa, daya a birnin Beijing mai suna “jami’ar koyon harsunan waje ta Beijing”, ita jami’a ce wadda ta fi shahara a nan kasar Sin wajen koyar da harsunan kasashen duniya, dayar kuma tana birnin Tianjin mai suna “jami’ar koyon harsunan waje ta Tianjin”.
Tambaya ta biyu: Me ya ba ki sha’awar koyon wannan harshe?
Lokacin da mutane suka ji na koyi Hausa a can China, sun rika mamakin cewa, ke kika zabi wannan harshe ko zaba maki aka yi? Kamar yadda ’yan Nijeriya su kan zabi sashen karatu, mu ma masu koyon harshen Hausa mun zabi wannan harshe ne da kanmu. Sai dai kuma akwai wata tambaya ta daban, wato akwai harsuna da dama a duniya, amma me ya sa na zabi wannan harshe?
Amsa:
Harshe wata gada ce ta yin mu’ammala, kuma yin magana da Hausawa, da harshen Hausa ya bayyana cewa, mu Sinawa muna mutunta al’adun Hausawa. Ta wannan hanya, Sinawa da Hausawa suna iya musanyar ra’ayi mai kyau.
Amma da farko, ban fahimci ma’anar koyon wani harshe na Afrika ba, sabo da Nijeriya na da nisa sosai daga China, ban san yaya Nijeriya take ba. Amma wannan ma’ana ta fito sosai bayan da aka tura aiki a matsayin wakiliyar sashen Husa na CRI a Najeriya.
Tambaya ta uku: Wace irin kafar yada labarai ce CRI, wadannan shirye-shirye wannan kafa ke watsawa a kowace rana?
Jama’a da dama sun nuna sha’awa sosai lokacin da suka ji ina aiki a sashen Hausa na CRI a birnin Beijing, hedkwatar kasar Sin. Sinawa da dama suna aikin yada labarai a harshen Hausa kowace shekara, lallai abin mamaki ne.
Amsa:
Gidan rediyon kasar China wato CRI (China Radio International) ya kasance wata kafar yada labarai ta kasar Sin da na Afirka, da na sauran kasashen duniya, kuma babban ofishinsa yana yammacin birnin Beijing. CRI wadda yake ma’aikata fiye da dubu 2, a kowace rana yana watsa labarai cikin harsuna 65, ciki har da harshen Hausa zuwa sauran bangarorin duniya. An kafa sashen Hausa na CRI ne tun a shekarar 1961, sannan ya fara watsa labaru da harshen Hausa a ran 1 ga watan Yunin shekarar 1963 a kowace rana. Muna tattara labarai daga sassan duniya daban-daban, muna fassara wadannan labarai zuwa harshen Hausa, wannan shi ne muhimmin aikinmu. Ban da wannan kuma, muna da shirye-shirye daban-daban kamarsu: Dogon bayani wanda ke mai da hankali kan wasu manyan labarai da suka faru a duniya. Shirin “In Ba Ku Ba Gida” shiri ne da ya shafi rayuwar mata da yara a duniya. Shirin “Sin Da Afrika” yana bayyana kan dangantaka tsakanin China da Afrika. Shirin “Allah Daya Gari Banban”, shi ma yana bayyana kan yadda al’ummomin kasar Sin suke samun sauye-sauye da ci gaba, da sauran shirye-shirye cikin harshen Hausa. Akwai wani muhimmin aiki a yau da kullum wato na neman labarai daga Nijeriya. Wakilin da sashin Hausa ya tura Nijeriya shi ke gudanar da wannan aiki.
Wace ce Amina Du?
Sunana Du Jing, ana kuma kira ni Amina a ofis, malamina malam Balarabe Shehu Illela dan asalin jihar Bauchi daga tarayyar Najeriya, shi ne ya ba ni wannan suna a jami’a. Akwai dalibai 10 a ajinmu, ciki har da maza 4 da mata 6. Na shiga sashen Hausa na CRI a shekarar 2009, kuma an tura ni zuwa Nijeriya a watan Octoba na shekarar 2016. A baya ba a taba tura mace zuwa Nijeriya ba, ni ce wakiliya ta farko da CRI ta tura zuwa Nijeriya.
Labarin Amina Du da Nijeriya!
Tun ina koyon harshen Hausa a shekarar 2004, na san wasu abubuwa da dama dangane da Nijeriya. A nan zan gabatar muku wadannan jerin labarai, zan bayyana muku bayanai game da zamana a Nijeriya, musamman ma yadda nake zaman rayuwa da gudanar da aiki a Nijeriya.
Labari na farko
Na isa Abuja hedkwatar Nijeriya ne a ranar 19 ga watan Oktoba na shekarar 2016, karo na farko da na taka kafa a Nijeriya, kuma ban san kowa ba, amma yayin da na gai da mutane da harshen Hausa,sai su kai ta mamaki, kuma sun tarbe ni hannu bibbiyu. Har wasu ma sun taimaka min sosai.
Ba da dadewa ba da isa na Abuja, sai na fara aiki gadan-gadan. A ran 25 ga watan Oktoba na 2016, aka yi bikin bude hedkwatar arewa maso yammacin kamfanin GEZHOUBA na kasar Sin a Abuja, mahalartar taro sun hada da karamin minista mai kula da wutar lantarki, gine-gine da gidaje Mustafa•Baba•Shehu, shugaban hukumar zirga-zirga ta kasar Boss•Mustafa da dai sauransu. Yayin da na nemi zantawa da Mista Boss ya yi mamaki sosai ganin yadda basiniya ta iya Hausa, ya kuma yarda mun yi hira.
Daga baya kuma, a ran 27 ga watan Oktoba, an yi bikin yada al’adun Sinawa a wasu makarantar Abuja dake yankin Garki na 10, inda dalibai da malamai fiye da 500 daga makarantu 16 suka halarci bikin, wadannan dalibai sun yi raye-raye da wake-waken Sinawa, lokacin da na gai da wadannan yara da Hausa sun yi mamaki inda suka kewaye ni, sun gaya mini cewa, suna kaunar al’adun Sinawa kwarai, kuma suna fatan wata rana za su ziyarci kasar Sin, domin ganewa idanunsu yadda kasar Sin dake bankon duniya take. Har ma wasu yaran sun yi tambayoyi kamar ’yan jarida, na rera musu wakar Sinanci kana na yi musu bayani game da kasar Sin. A karshe dai wata yarinya ta tambaye ni, shin gashina na gaskiya ne ko jabu, tana son ta tabo gashina, na yarda, ta tabo gashina ta yi mamaki ta ce: gashin yana da santsi kamar siliki. Wadannan yara suna matukar son fahimtar kasar Sin da ma Sinawa, kamar yadda suka taba gashina, suna son wata rana su ga kasar Sin da idonsu, mu ma masu yada labarai dake magana da harshen Hausa muna fatan zama wata gada, shirye-shiryenmu wata hanya ce ta yadda masu sauraro za su kara fahimtar kasar Sin.
Sabo da yadda na ziyarci wurare daban-daban, labarin Basiniya da ta iya Hausa da ta zo nan Abuja, ya yadu zuwa wurare daban-daban. Gidan rediyon Aso FM da gidan talabijin na kasa dake Najeriya wato NTA sun gayyace ni don zantawa da ni. Yayin hirarmu, wani muhimmin abin da muka ambata shi ne mu’ammala da mutunta juna.

Wani jagoran shiri ya yaba sosai ga ayyukan da sashin Hausa na CRI ya gudanar a wadannan shekaru, kuma yana fatan karin masu yada labarai na kasa da kasa su yi koyi da harsunan Afrika don zuwa kasashen Afrika kamar yadda wakilan CRI suke yi. Da na ji haka, na yi tunanin cewa, a yayin wani bikin da aka yi mai taken “Sada zumunci tsakanin matasan Sin da Afrika” a watan Yuli na shekarar 2016, na taba zantawa da wani babban jami’in Najeriya inda ya fadi mini cewa: “Sin da Nijeriya na bukatar mu’ammala matuka, kuma harshe ya zama gadar yin mu’ammala, ina farin ciki sosai da ganin Sinawa da suka iya Hausa, abin da ya kasance matakin girmama al’adun Hausawa. Har ma wasu matasan Hausa da ba su kai kamar Sinawa fahimtar al’adun Hausa ba, abin da ya ba ni karfin gwiwar cewa, ya kamata mu mai da hankali wajen kiyaye al’adunmu, kuma ina fatan matasan Nijeriya za su kara himma da gwazo wajen koyon Sinanci da adabin Sinawa, ta yadda jama’ar kasashen biyu za su iya mu’ammala da juna sosai.”
Babban aikin gidan rediyon kasar Sin (CRI) shi ne gabatarwa duniya bayanai game da kasar Sin da kuma Sinawa abubuwan dake faruwa a sassan duniya, yin amfani da harsuna daban-daban shi ne muhimmin yakini kara fahimta da tuntubar juna. Yanzu CRI tana yada labarai a ko wace rana cikin harsuna 65 zuwa ga dukkan bangarorin duniya.
Saboda wannan muhimmiyar manufa ce, na ci gaba da kokarin aikina a Najeriya, zan gabatar muku labarai game da aiki da zaman rayuwata a Najeriya a karo mai zuwa.
Daga karshe dai, ina fatan kuna lafiya a Najeriya kamar yadda nake nan Beijing, kasar Sin. Kuma ina fatan za ku rika sauraran shirye-shiryenmu da kuma karanta labaru a shafin intanet na http://hausa.cri.cn. Sannan za ku iya turo mana wasiku a cikin e-mail: hausa@cri.com.cn. (Amina Du, ma’aikaciyar sashen Hausa na CRI)


Advertisement
Click to comment

labarai